25 Agusta 2017 - 15:10
Shugaban Nigeria Ya Rattaba Hannu Kan Yerjeniyoyi Na Yakar Cin Hanci Da Rashawa

Shugaban Nigeria Mohammadu Buhari ya sanya hannu kan wasu yerjejeniyoyi wadanda suka hada da na yaki da cin hanci da rashawa, kudaden haraji da kuma kare hakkin mallaka na masu ayyukan fasaha na kasa da kasa.

Shafin labarai na sahara reporters ya bayyana cewa shugaban ya sanya hannu a kan wadan nan yerjejeniyoyi ne a jiya Alhamis kuma ya bukaci dukkan ma'aikatu da cibiyoyin da abin ya shafa su fara aiwatar da yerjejeniyoyin. 

A cikin yerjeniyoyin dai akwai ta fahintar juna tsakanin Nigeri da Haddadiyar Daular Larabawa na taimakawa juna kai yaki da aikata laifuffuka, musayar fursinoni, da kuma mika wadanda ake zargi da laifi zuwa gwamnatocin kasashensu. Har'ila yau yerjejeniyoyin sun hada da na batun kudaden fiti tsakanin kasashen takbkin chadi da na wasu kasashen Afrika.  Daga karshe akwai batun kare hakkin masu ayyukan fasaha na fina-finai da wake wake.da sauransu.288